ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samar Da Cikakkun Cibiyoyin Kiwon Lafiya Ga Al’ummar Duniya

by Leadership Hausa
4 years ago
Lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa, samar da cikakkiyen tsari na kiwon lafiya ga al’umma zai kai ga samar da al’umma masu koshin lafiya da za su iya bayar da gudmmawar su ga cigaba yankunan da suka samu kansu, a kan haka ne hukumar ta tsayu wajen gudanar da bukin ranar lafiya ta duniya da aka ware kowacce ranar 12 ga watan Disamba na kowacce shekara, wannan wata dama ce na jawo hankalin masu ruwa da tsaki a kan halin da harkar kiwon lafiya take ciki a sassan duniya.

Taken bikin wannan shekarar shi ne, “Samar Da Duniyar Da Muke Bukata: Samar Da Cikakkiyar Lafiya Ga Kowa Da Kowa.” An karfafa bukatar samar da daidaito, aiki da gaskiya da kuma muhalli mai kyau tare da zuba jari mai inganci don samar da hukumomin lafiya ingantattu da za su iya tabbatar da ganin lafiyar al’ummar duniya tana gudana ba tare da wata matsala ba.

  • Zan Bayyana Dan Takarar Da Zan Mara Wa Baya A Janairu – Wike
  • An Kammala Kashin Farko Na Layin Dogon Jihar Lagos

Shirin samar da lafiya ga al’ummar duniya zai tabbatar da gina cibiyoyin lafiya masu inganci a sassan duniya tare da bude kofar cibiyoyin ga kowa da kowa. Samar da kiwon lafiya ga al’umma yana da nasaba ga ci gaba duniya gaba daya. A irin wannan ranar ne ana kwatanta yadda cibiyoyin lafiya suke a sassan duniya da nufin irin bambancin da ake samu a tsakaninsu don hakan ya zama darasi mahukunta ta haka za su himmatu wajen an kara bayar da kokari don samun al’umma masu cikakkiyar lafiya a sassan duniya.

ADVERTISEMENT

Saboda muhimmancin samar da cikakkiyar kiwon lafiya ga al’ummar duniya a halin yanzu an sanya lamarin a cikin muradun karni da ake fatan cimma a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2030, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi. A kasashe da dama samar da cikakken tsarin kiwon lafiya yana neman ya fi karfin talakawa a cikin al’umma.

Babban ginshikin a tsarin samar da kiwon lafiya shi ne samar da ruwa a kan haka ne kungiyar ‘WaterAid’ ta bayar da rahoton cewa, harkar kiwon lafiya ta kasashe da dama ta rushe ne saboda yadda aka kasa samar da ingantaccen ruwan sha, haka ma an kasa samar da wutar lantarki ga al’umma yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Hakanan kuma Hukumar Lafiya ta Duniya da UNICEF sun bayar da rahoto a shekarar 2015 cewa, kashi 38 na asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da rahoton ya karkacde basu da hanyoyin samun cikakkken ruwan sha, kashi 35 kuma basu da ruwan da masu mu’amala da su za su samu isasshen ruwan da za su wanke hannu da shi don kariya daga cututtuka yadda ya kamata. Rahoton ya kuma lura da cewa, in har jami’an kiwon lafiya basu iya tsaftace harabobin asibiti yadda yakamata to kokarinsu na bayar da cikakkiyar kulawa yana cikin gargara kenan.

Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, tsarin nan na WASH wanda hukumar WHO da UNICEF ke daukar nauyi suna cikin tsarin nan na Majalisar Dinkin Duniya na ‘UN’s Global Action Plan” na tabbatar da ganin dukkan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin duniya suna samun isashen ruwa yadda yakamata don gudanar da ayyukansu nan da shekarar 2030.

Yana kuma da muhimmanci a lura cewa, samar da ingantaccen kiwon lafiya a duniya a bu ne daya shafi kowa da kowa, kuma a wannan lokacin ne ya fiye kowanne lokaci yakamata a tabbatar da dukkan cibiyoyin kiwon lafiyarmu sana samun kulawa yadda yakamata. Cutar Korona da aka fuskanta a fadin duniya ta zama wani gwaji ga cibiyoyin kula da lafiyar mu. Hankalin shugabanin ya koma a kan bukatar tabbatar da ganin cibiyoyin kiwon lafiyan mu suna aiki yadda yakamata don fuskantar ire-iren wannan matsalar a nan gaba.

Haka kuma wasu na ganin shirin samar da kiwon lafiya kamar wani hakki ne da yakamata kowa ya samu amma wasu kuma na ganin lamarin a matsayin wata haja, saidai gaba daya lamarin samar da kiwon lafiya ga al’umma ya tashi daga wani abin da ba a dauka da muhimmanci ba zuwa wani abin da ya zama gaskiya musamman ma a kasashen duniya da suka cigaba.

Amma kuma ga wasu al’umma masu yawa, musamman na kasashe matalauta hakar sammar da kiwon lafiya harkan kamar a mafarki.

Rahoton hukumar WHO suka bayyana cewa, akalla rabin al’ummar duniya basu da zarafin samun cikakken kiwon lafiya kamar yadda shirin muradun karni SDGs ya tabbatar, da kuma kudurin majalisar dinkin duniya ya nema.

Wani lamari mai muhimmanci game da shirin samar da kiwon lafiya ga al’ummar duniya shi ne bukatar da ake yita sai mutane sun biya kudin kiwon lafiyar su wanda haka yana kara tura akalla mutum miliyan 100 ne zuwa cikin kangin talauci a duk shekara ciki kuma akwai ‘yan Afrika fiye da mutum miliyan 11.

Kashi 77.2 a cikin dari na ‘yan Nijeriya na cigaba da dogara ne da sayen magani a kemis a duk lokacin da suke fama da rashin lafiya. Shirin samar da kiwon lafiya ga al’umma yana fuskantar matsaloli iri daya musamman a Nijeriya da sauran kasashen Afrika, cikin matsalolin akwai yadda aka fuskanci matsalolin da cutar korona ta haifar musamman daga hukumomi.

Amma kuma wasu mastalolin lamari ne da ta shafi duniya gaba daya, wadanda suka hada da yadda aka rika tattara bayanai, da zuba jari da batun samar da kwararru wadanda za su yi aikin da ya kamata na ganin an cimma burin da aka sa a gaba.

Haka kuma masana sun tabbatar da cewa, in har ana son cimma shirin samar da ingataccen tsarin kiwon lafiya ga al’ummar duniya dole ne a inganta asibitocinmu, a kuma horas da ma’aikatan lafiya da kara yawan cibiyoyin kiwon lafiyar a sassan Afrika.

Lafiya
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Fara Raba Muhimman Kayayyakin Zabe Da Kone-konen Ofishoshin INEC: Ga Koshi Ga Kwanan Yunwa

Fara Raba Muhimman Kayayyakin Zabe Da Kone-konen Ofishoshin INEC: Ga Koshi Ga Kwanan Yunwa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.