Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG a takaice, ya gudanar da gwaji na biyu, na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa a jiya Talata, inda aka kara inganta shirye-shiryen.
Shirye-shiryen dai sun bayyana jigon bikin na murnar shiga sabuwar shekara, da karfafa wa al’umma gwiwar kokartawa, don isar da fatan alheri na tabbatar da bunkasuwar kasar, da ma lafiyar al’umma cikin sabuwar shekara.
Bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, Sinawa za su shiga sabuwar shekararsu a ranar 22 ga watan nan da muke ciki, kuma CMG ya kan gabatar da shirye-shiryen bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa a kowace shekara, a jajebirin ranar sabuwar shekarar. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp