Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin kai ziyarar aiki a kasar Malaysia, a ranar 12 ga watan da muke ciki bisa agogon wurin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, ya kaddamar da nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin masu inganci a Kuala Lumpur dake Malaysia. Za a kuma watsa shirye-shirye guda 10 da CMG ya shirya a muhimman kafafen yada labaru na Malaysia, misali shirin “Ra’ayoyin Xi Jinping kan al’adu” da na “Kawar da talauci”.
Ban da hakan, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce, nuna shirye-shiryen da ake yi a wannan karo zai sa kaimi ga mu’ammalar al’adu tsakanin Sin da Malaysia, ana fatan ta hanyar watsa wadannan shirye-shirye masu inganci, masu kallo na Malaysia za su kara fahimtar al’adu, da al’ummar Sinawa da yanayin da kasar Sin ke ciki a sabon zamani.
A ran nan, CMG ya kaddamar da nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin masu inganci a Kambodia a birnin Phnom Penh dake kasar.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp