Yau Laraba, ranar 27 ga wata, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da wani taron kaddamar da wasu sabbin shirye-shiryen bidiyo masu amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, a dandalin kasashen Asiya na Boao, inda masu kallo suka samu damar kallon sabbin shirye-shiryen bidiyo na AI da dama da CMG ke samarwa, wanda ke bayyana tarin littattafan gargajiya na kasar Sin, da tatsuniyoyin gargajiya na kasar. ‘Yan jaridu daga kasashe 26 na duniya sun shaida idanunsu “gamuwar ban mamaki” tsakanin kyawawan al’adun gargajiyar kasar Sin da fasahar AI.
A dandalin Boao na bana, fasahar AI ta zama babban batu da mahalarta taron ke tattaunawa a kai. Masu karbar bakuncin taron sun shirya tattaunawa da dama kan juyin-juya-halin kimiyya da fasaha, da abubuwan da fasahar AI ta samar, da gudanar da harkokin duniya ta hanyar fasahar AI, wadanda suka ja hankali sosai. (Mai fassara: Bilkisu Xin)