Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira wani taron manema labarai a yau Alhamis da safe, inda aka yi karin haske kan bukukuwan baje kolin hotuna da kayayyaki da nagartattun fina-finai da shirye-shiryen bidiyo da sauran ayyukan nuna fasahohi, don murnar cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin sojojin Japan da na kin tafarkin murdiya.
Mataimakin shugaban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, Wang Xiaozhen ya bayyana cewa, CMG ta yi iyakacin kokarin samar da jerin fina-finai da shirye-shirye masu dimbin yawa na harsuna da yawa a dukkan dandaloli, don bayyana ma’anar nasarar da Sinawa suka samu a yakin kin harin sojojin Japan, da babbar gudunmawar da Sinawa suka bayar na yaki da tafarkin murdiya a duniya, ta yadda aka samar da halaye masu kyau wajen tunawa da wannan babbar rana.
Wadannan fina-finai da shirye-shirye sun bullo da labaran tarihi da ba a taba watsa su ba, kuma CMG ta yi amfani da fasahar zamani ta yadda za su kara jawo hankulan masu kallo. Mista Wang ya kara da cewa, CMG za ta yi amfani da fifikonta na yada labarai ta harsuna 82 a tasoshinta 192 a duniya, don bayyana wadannan labarai masu jan hankali dangane da yadda Sinawa suka yi yaki da harin sojojin Japan.
Ban da wannan kuma, a gun taron manema labaran, an ce, hukumar sashen yayyata ayyuka na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido da CMG da kuma sashi mai kula da harkokin siyasa na kwamitin soja na kwamitin kolin JKS da birnin Beijing, za su gabatar da bikin murnar cika shekaru 80 da samun wadannan nasarori cikin hadin gwiwa da daren ran 3 ga watan Satumba mai zuwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp