• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CMG Za Ta Nunawa Duniya Yadda Ake Hadin Gwiwar Moriyar Juna

by CGTN Hausa
2 years ago
CMG

Gabanin babban taron kasa da kasa dangane da hadin gwiwa bisa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya dake cika shekaru 10 a bana, babban rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin CMG, ya kaddamar da hadin gwiwa da kafofin watsa labarai na kasashen dake aiwatar da shawarar.

Hakika waka a bakin mai ita ta fi dadi. Wannan hadin gwiwa zai bada damar bayar da cikakku kuma sahihan labaran kasar Sin da ainihin yanayin da ake ciki dangane da shawarar kamar yadda ya kamata, ga al’ummomin duniya. Haka kuma, zai taka rawa wajen wayar da kan kasashen duniya game da irin alfanun shawarar da ayyukan da ake aiwatarwa a karkashinta.

  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jadda ‘Yancin Dan Adam Wajen Samun Kiwon Lafiyar Kwakwalwa
  • Sin Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jirage Marasa Matuka Da Aka Kai Kan Wata Makarantar Soji A Syria

A ganina, kasar Sin ba ta samu yabon da ya kamata game da ayyuka da tallafi da shawarwari da ma dabarun samar da ci gaba da zaman lafiya da take gabatarwa a duniya, saboda yadda wasu kasashe suka dukufa wajen shafa mata bakin fenti. A yanzu, kasar Sin da ta jagoranci gabatar da shawarar tare da raya ta, za ta samu damar bayar da labari da bakinta ta hannun CMG, yayin da kafofin watsa labarai na kasashen da shawarar ta shafa, za su watsa wadannan sahihan labarai da bayanai ga al’ummominsu, lamarin da zai sa jama’ar kasa da kasa su kyautata fahimtarsu kan kasar Sin.

Kasancewar kafofin yada labarai, matsayin masu ilmantarwa da wayar da kan al’umma, wannan hadin gwiwa zai taimaka gaya wajen kore jita-jita da dukkan wasu labarai na karya da ake yadawa. Ta hakan ne kuma, al’ummomin duniya za su gane matsayin kasar Sin na mai neman daidaito da moriyar juna tsakanin kasa da kasa dake da burin gina al’umma mai makoma ta bai daya.

Da yake gabatar da jawabi, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce CMG ta sa hannu kan yarjejeniyoyin watsa labaru da kafofin yada labaru 682 daga kasashe 15 domin yada shirye-shirye gane da shawarar. Wannan gagarumin ci gaba ne la’akari da cewa, cikar shawarar shekaru goma ta nuna cewa tana kara bunkasa, don haka akwai bukatar kara wayar da kai game da burika da manufofin kasar Sin na hadin gwiwa, domin al’ummun duniya su gane cewa, yanzu an shiga wani babi na hadin gwiwar moriyar juna bisa adalci da daidaito, maimakon wanda aka saba gani na cin nasara daga faduwar wani bangare.

LABARAI MASU NASABA

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Ko shakka babu, ina da yakinin bisa irin jajircewarta, CMG za ta cimma burinta, kuma duniya za ta fahimci ainihin kasar Sin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE
Daga Birnin Sin

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Next Post
Gwamnatin Kasar Sin Ta Amince Da Takardun Ba Da Tabbacin Zaman Al’umma Da ’Yancin Mallakar Fasaha

Gwamnatin Kasar Sin Ta Amince Da Takardun Ba Da Tabbacin Zaman Al'umma Da ’Yancin Mallakar Fasaha

LABARAI MASU NASABA

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Yadda Ake Miyar Margi

Yadda Ake Miyar Margi

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.