A gobe da dare misalin karfe 8 ne babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin CMG zai watsa shirin nishadantarwa na murnar bikin Zhongqiu ga masu kallo a duk fadin duniya.
Ranar 6 ga watan Oktoban bana, rana ce ta bikin tsakiyar yanayin kaka, wato bikin Zhongqiu da Sinanci. A kan yi wannan biki a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiransa bikin Zhongqiu. Har ila yau kuma, a wannan rana da dare, wata ya fi cika da’irarsa da kuma zama mai cikakken haske, ta yadda a lokacin da Sinawa suke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, sabo da haka Sinawa sun dauki bikin na Zhongqiu a matsayin bikin haduwar iyali. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp