Kwanan baya, wasu rahotanni na nuna cewa, wai jakadan kasar Amurka dake kasar Sin R. Nicholas Burns ya ce, kasar Sin ba ta da shirin yin haɗin gwiwa da Amurka a fannin binciken duniyar wata. Dangane da wannan batu, kakakin hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin wato CNSA Xu Hongliang ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da ayyukan sararin samaniya da yin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana. Kuma tana fatan yin shawarwari da hadin gwiwa da kasashen duniya bisa tushen adalci da cimma moriyar juna, yin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana, da nuna fahimtar juna da neman ci gaba, ta yadda za a ba da kwarin gwiwar karfafa dunkulewar bil Adama ta fuskar nazarin harkokin sararin samaniya.
Kasar Sin tana mai da hankali matuka a fannin hadin gwiwar binciken harkokin sararin samaniya, kuma tana kiyaye ra’ayin bude kofa wajen yin shawarwari da kasar Amurka kan ayyukan da abin ya shafa. Kana, kasar Sin tana maraba da masanan kasar Amurka da ma sauran kasashen duniya, da su neman izni ta hanyoyin da suka dace, bisa bayanin da kasar Sin ta fidda, a duk lokacin da suke son gudanar da nazari kan samfurorin da ’yan sama jannatin kasar Sin suka dawo da su duniyarmu daga duniyar wata.
- Sin Za Ta Daidaita Haraji Kan Hajojin Da Ake Shige Da Ficen Su A 2024
- Sin Ta Kara Tallafin Kudi Don Maido Da Wuraren Kiyaye Ruwa A Yankunan Da Girgizar Kasar Ta Shafa
Kasar Sin ba ta taba fidda wata takarda ko manufar kin hadin gwiwa da kasar Amurka ba. Amma, akwai masana da dama na kasashen duniya da suka taba yin kira ga kasar Amurka da ta kawar da dokar “Wolf Act”, wadda ta hana yin hadin gwiwa da kasar Sin kan ayyukan nazarin sararin samaniya.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na fatan kwararrun kasar Amurka za su taimaka wajen soke wannan doka, ta yadda za a gudanar da nazari kan sararin samaniya cikin hadin gwiwa, da ba da karin tallafi ga al’ummar kasashen duniya. Hakika kasar Sin tana fatan habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen duniya wajen aiwatar da ayyukan nazarin samarin samaniya.
Sannan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ma ya ce, har kullum Sin na maraba da Amurka a fannin musaya da hadin gwiwar ayyukan da suka shafi binciken sararin samaniya. Wang ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Juma’ar nan.
Wasu rahotannin baya bayan nan sun hakaito jakadan Amurka a kasar Sin Robert Nicholas Burns, na cewa wai Sin ba ta da niyyar yin hadin gwiwa da Amurka a fannin binciken duniyar wata, kuma fannin zai kasance wani fage guda ga kasashen biyu.
Game da hakan, Wang Wenbin ya ce gwamnatin kasar Sin ta sha bayyana aniyarta ta bunkasa bincike, da amfani da sararin samaniya ta hanyoyin zaman lafiya, kuma a shirye take ta gudanar da musaya, da hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya bisa daidaito, da cimma moriya tare, da kuma bunkasa fannin tare da juna, da ingiza gina al’umma mai makomar bai daya a fannin binciken sararin samaniya.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, idan har da gaske ne Amurka na son ingiza musaya, da hadin gwiwa tare da Sin a wannan fanni, to kamata ya yi ta kawar da dokokin ta dake yin tarnaki ga hakan, ta kuma dakatar da bayyana kalamai marasa dacewa, kana ta aiwatar da matakai na zahiri, na kawar da duk wani shinge dake dakile hadin gwiwar sassan biyu. (Masu Fassarawa: Maryam Yang, Saminu Alhassan)