A ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, a harabar sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano, wani ɗalibin Jami’ar Bayero mai suna Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin shiga kundin tarihin duniya na Guinness a fannin fentin fuska mafi yawa cikin minti uku. Da goyon bayan kamfanin Indomie, Collins ya fente fuskar mutum 17 a cikin ƙasa da minti 3, lamarin da ya karya kambun da Emilia Zakonnova ta kafa na fentin fuskar mutum 12 a ranar 30, ga Yuli, 2025.
Ga yadda sakamakon yunƙurin shiga kundin tarihin nasa ya kasance:
- PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai
- Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Gwamnatin Amurka Ta Tsayar Da Ayyukanta
Gwaji na 1: Minti 2 da daƙiƙoƙi 40 a fuskar mutum 17
Gwaji na 2: Minti 2 da daƙiƙoƙi 50 a fuskar mutum 17
Gwaji na 3: Minti 2 da daƙiƙoƙi 55 a fuskar mutum 20.
Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan Indomie, domin mu kafa tarihi.”
A wajen Collins, fentin fuska ba nishaɗi ba ne kaɗai ba, fasaha ce da ke bayyana fikira da ƙirƙira. Ƙoƙarinsa ya haskaka wa duniya irin baiwar da matasa ’yan Nijeriya suke da ita a idon duniya.
Kamfanin Indomie, ya jima yana bayar da gudummawa da goyon baya a fannin ƙirƙira da ilimi a tsakanin matasa, kamfanin ya bayyana farincikinsa da alfaharinsa na ɗaukar nauyin Collins.
Collins ya bayyana cewa, “Ina son na zama sanadin sanya Kano da Nijeriya a idon duniya, domin mu nuna muna da ƙwararrun mutane da za su iya fito da fasahar su a idon duniya. Yau na yi fentin fuska 17 a cikin minti 2 da sakan 40, wanda ya zarta abin da aka ba ni na yin fentin fuskar mutane 13. Ina gode wa Indomie da iyalina da abokaina da masu yi min fatan alheri.”
Daga cikin waɗanda suka halarci taron, wani ɗalibin BUK, Sulaiman Haruna, ya ce: “Ina addu’ar Collins ya yi nasara saboda ya nuna bajinta sosai.” Wani shaidar gani da ido a taron, Jimoh Momoh, ya yaba da ƙoƙarinsa yana mai cewa Collins zai iya kafa tarihin. Wata ɗaliba mai suna Aisha ma ta nuna mamakinta kan lamarin Collins ta kuma bayyana goyon bayanta da fatan ganin Collins ya samu nasara.
A yanzu da dai bayan kammala wannan taron kallo ya koma sama, kowa na jiran mataki na gaba daga Guinness World Records. Da zarar mahukunta sun kammala tantance ƙoƙarin Collins, suka tabbatar da nasararsa, zai shiga cikin jerin masu rike kambun duniya, lamarin da zai ƙara wa matasan Nijeriya ƙwarin guiwa da ƙarfafa fasaha a ƙasa baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp