Ƙungiyar Real Madrid ta ƙi halartar atisayen motsa jiki da taron manema labarai na wasan ƙarshe da za ta ƙara da Barcelona a gasar Copa del Rey, wanda aka shirya ranar Juma’a.
Hakan ya biyo bayan ƙorafin da ta yi kan alƙalin wasan da aka naɗa, Ricardo de Burgos Bengoetxea.
- Shin Manchester United Za Ta Iya Lashe Kofin Europa League?
- Fita Daga PDP: Babu Wani Abu Da Zai Cutar Da PDP, Jam’iyyarmu Za Ta Ƙara Haɓaka – Bukola Saraki
Real Madrid ta bayyana cewa tana fushi da alƙalin wasan saboda ya soki yadda kulob ɗin ke caccakar alƙalan wasanni a Laliga.
Saboda haka, Real Madrid ta roƙi hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) da ta canza alƙalin kafin wasan ƙarshe da za a buga ranar Asabar.
Ƙungiyar ta kuma sanar da cewa ba za ta shiga atisayen wasannin ko wani taron da ya shafi shirye-shiryen wasan ba, har sai hukumar ƙwallon ƙafa ta ba ta amsa buƙatarta na sauya alƙalin.
A cikin wannan mako, gidan talabijin na Real Madrid ya fitar da wani faifan bidiyo da ke sukar lamirin alƙalin da zai hura wasan.
A baya kuma, Real Madrid ta taɓa rubuta wasiƙa a watan Fabrairu tana ƙorafin cewa alƙalai a Sifaniya ba sa musu adalci.
Haka kuma, a watan Oktoban 2024, kulob ɗin ya ƙaurace wa bikin bayar da kyautar Ballon d’Or saboda rashin bai wa ɗan wasanta Vinicius Junior kyautar gwarzon ɗan kwallon duniya.