Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da cewa cutar mashako ta ‘Diphtheria’ ta barke a jihar har ta kashe wasu dalibai guda biyu a karamar hukumar Jama’are da ke jihar.
Shugaban hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi (BSPHCDA), Dakta Rilwanu Muhammad ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Laraba.
Ya ce, cikin samfuri na gwaje-gwaje da aka yi wa mutum 58, an tabbatar mutum biyu sun mutu sakamakon cutar.
A cewarsa, hukumar ta tashi tsaye wajen ganin ta dakile yaduwar cutar, ya na mai cewa za a yi rigakafi ga yara domin kariya daga cutar.
Rilwanu ya kara da cewa gwamnatin jihar ta umarci a rufe dukkanin makarantun da aka samu bullar cutar a matsayin matakan kariya.
Ya kara da cewa duk wata makarantar da aka tabbatar da bullar cutar a cikinta to gwamnati za ta rufe domin kariya.
“Muna son mu yi wa yara rigafi a cikin sati shida, kuma rigakafin kyauta ne,” ya shaida.
Ya misalta rasuwar daliban a matsayin abun damuwa matuka. Ya ce, suna kan kokarinsu wajen dakile yaduwar cutar a halin yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp