Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero.
LEADERSHIP ta fahimci cewa an kama Ajaero da safiyar ranar Litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
- Babu Ranar Komawa Kananan Makarantu A Jihohin Kano Da Edo
- Afrika Ta Kudu Na Neman Hadin Gwiwa Da Sin Wajen Zamanantar Da Kanta
Talla
Ajaero na shirin shiga jirgi zuwa Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance a yayin da DSS ta kama shi.
Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, an bukaci Ajaero da ya halarci taron kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da za a yi a kasar Ingila ranar Litinin.
Sai dai, ba a bayyana cikakken bayani da dalilin kama shi ba, majiya mai tushe ta ce an mika Ajaero ga hukumar leken asiri ta kasa, NIA.
Cikakken bayani na tafe
Talla