Wasu mata, a yau Litinin sun fito kan titi tare da yin cincirindo a kan titin Kpagungu da ke Minna-Bida cikin babban birnin jihar Neja, inda suke gudanar da zanga-zangar kokawa kan halin matsi da yunwa da tsadar rayuwa da suke fama da shi.
Matan dauke da alluna da aka rubuta “Ba abinci, yunwa na kashe mu” sun bukaci a samar musu da ingantacciyar rayuwa tare da lalubo musu magita kan tsadar rayuwa da ta addabe su.
Sun zargi masu rike da mukaman siyasa da rashin kula da halin da suke ciki tare da koka wa da rashin samun damar cin abinci koda sau daya a rana.
Talla