Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, maimakon Litinin kamar yadda aka tsara tun da farko.
Tsohon shugaban ƙasa, Buhari ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan, a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
- DA ƊUMI-ƊUMI: Wani Gidan Bene Mai Hawa Uku Ya Rufto, Ya Kashe Mutum 4, Da Jikkata 7 A Kano
- Shugaban ECOWAS Julius Bio, Ya Yi Wa Tinubu Da ‘Yan Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Buhari
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a filin jirgin sama na Umaru Musa Yaradua da ke Katsina a ranar Litinin.
Ya ce, “Mun tuntuɓi iyalinsa da kuma mutanen da ke tare da shi a Landan. Mun yanke shawarar za a kawo gawarsa Katsina da misalin ƙarfe 12 na rana, sannan a yi jana’izar sa a Daura da misalin ƙarfe 2 na rana.”
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin a madadin gwamnati da al’ummar jihar Katsina, yana mai bayyana Buhari a matsayin uban ƙasa da ya ke da muhimmin tarihin kan riƙo da gaskiya da amana.
An ƙara tsaurara matakan tsaro a Daura da kewaye yayin da ake shirin gudanar da jana’izar Buhari saboda ana sa ran halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasa da za su halarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp