A watan Satumban 2025, hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 18.02 bisa 100 idan aka kwatanta da na watan Agustan 2025 inda ya kai kashi 20.12 bisa 100, kamar yadda sabbin bayanai da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna.
Alkaluman da aka fitar a ranar Laraba ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a watan Satumban 2025 ya ragu da kashi 2.1 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Agustan 2025.
A lissafin shekara-shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 14.68 bisa 100 a maimakon kashi 32.70 bisa 100 a watan Satumban 2024.
A ɓangaren hauhawar farashin abinci a watan Satumba na 2025, ya dawo kashi 20.9 cikin 100 a maimakon kashi 37.77 cikin 100 a cikin watan Satumban 2024