Jam’iyyar PDP ta hukunta Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ta hanyar korarsa daga jam’iyyar, yayin da ake gudanar da Babban Taron Jam’iyyar na Ƙasa a Ibadan, Jihar Oyo.
Jam’iyyar ta kuma kori tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da kuma tsohon Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa da aka dakatar, Sanata Samuel Anyanwu.
- An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
- Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso
Sauran da jam’iyyar ta kora sun haɗa da tsohon Lauyan Jam’iyyar na Ƙasa, Kamaldeen Adeyemi Ajibade (SAN); Sanata Mao Ohuabunwa; George Turner; Hon. Umar Bature; da Alaba Turnah, da sauransu.
Tsohon Mataimakin Shugaban PDP (daga yankin Kudu), Cif Olabode George ne, ya gabatar da shawarar korarsu, inda ya bayyana cewa suna yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.
Shawarar ta samu amincewar wakilan da suka halarci taron.













