Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mai barin gado ya mika ragamar shugabancin hukumar a hukumance ga Misis May Agbamuche-Mbu, wacce za ta zama shugabar riko.
Taron ya gudana ne a ranar Talata yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kwamishinonin zabe a hedikwatar INEC da ke Abuja.
- Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa
- Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya
Agbamuche-Mbu, wacce itace kwamishina mafi dadewa a hukumar zabe ta kasa INEC, za ta ci gaba da kula da harkokin hukumar zabe har sai an nada sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta.
Da yake sanar da ajiye aikin, Farfesa Yakubu ya bukaci ma’aikatan hukumar da su ba da cikakken goyon baya da hadin kai ga mukaddashiyar shugaban hukumar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Mrs. Agbamuche-Mbu, ƙwararriya ce kuma lauya, tana cikin tawagar gudanarwar hukumar ta INEC tun lokacin da aka naɗa ta a matsayin kwamishina ta ƙasa, kuma ana sa ran za ta ci gaba da kula da shirye-shiryen hukumar.