• English
  • Business News
Friday, June 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Ɗumi-ɗuminsa: Iran Ta Tabbatar Da Rasuwar Shugabanta Raisi A Hatsarin Jirgin Sama

by yahuzajere
1 year ago
in Da ɗumi-ɗuminsa
0
Da Ɗumi-ɗuminsa: Iran Ta Tabbatar Da Rasuwar Shugabanta Raisi A Hatsarin Jirgin Sama
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Rahotannin da muke samu da ɗumi-ɗuminsa sun tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasar Iran Ebrahim Raisi ya rasu bayan wani hatsarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi.

Wani jami’in gwamnatin ƙasar ta Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewa shugaban kasar ya rasu ne tare da ministan harkokin waje Hossein Amirabdollahian.

Har ika yau daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin, akwai Gwamnan Gabashin Lardin Azerbaijan, Malek Rahmati da Limamin Tabriz, Imam Mohammad Ali Alehashem da shugaban jami’an tsaron tawagar da babban dogara shugaban ƙasar da shugaban ma’aikatan jirgin da kuma matuƙa jirgin su biyu.

Ana sa ran a rantsar da mataimakin shugaban ƙasar ta Iran na farko, Mohammad Mokhber a matsayin sabon shugaban ƙasa.

Masu hasashe dai na bayyana fargabar mutuwar Shugaba Raisi na iya sake jagula rikicin gabas ta tsakiya wanda Isra’ila ke ci gaba da kashe Falasɗinawa tun bayan ƙaddamar da hare-haren a yankin Gaza, saboda nuna ɗan yatsa da za a yi ga Isra’ila da aminiyarta Amurka saboda yadda sa-in-sa ta ɓarke a tsakanin Iran da Isra’ila bayan harin da Isra’ila ta kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran a Siriya da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran.

Labarai Masu Nasaba

Tinubu Ya Soke Ziyarar Kaduna, Zai Tafi Benuwe Saboda Rikice-Rikice

An Kama Mata Da Mahaifiyar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ado Aliero A Saudiyya

Ita ma Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare da jirage marasa matuka kimanin 300 inda suka lalata wasu wurare na sojoji a Isra’ila yayin da kuma Ingila da Amurka suka yi iƙirarin sun tare galibin jirage da makaman da Iran ta harba a kan Isra’ila.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaGabas ta TsakiyaIranIsra'ilaMutuwaRasushugaban ƙasa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tinubu Ya Yi Jimamin Mutuwar Oba Yusuf Oyekanmi

Next Post

Kashim Shettima Ya Ƙaddamar Da Shirin ASSEP A Bauchi

Related

Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci
Da ɗumi-ɗuminsa

Tinubu Ya Soke Ziyarar Kaduna, Zai Tafi Benuwe Saboda Rikice-Rikice

2 weeks ago
An Kama Mata Da Mahaifiyar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ado Aliero A Saudiyya
Da ɗumi-ɗuminsa

An Kama Mata Da Mahaifiyar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ado Aliero A Saudiyya

1 month ago
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?
Da ɗumi-ɗuminsa

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

1 month ago
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma
Da ɗumi-ɗuminsa

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

2 months ago
Gobara Ta Tashi A Barikin Sojoji A Borno, Bama-bamai Sun Fashe
Da ɗumi-ɗuminsa

Gobara Ta Tashi A Barikin Sojoji A Borno, Bama-bamai Sun Fashe

2 months ago
Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N835 Kan Kowace Lita
Da ɗumi-ɗuminsa

Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N835 Kan Kowace Lita

2 months ago
Next Post
Kashim Shettima Ya Ƙaddamar Da Shirin ASSEP A Bauchi

Kashim Shettima Ya Ƙaddamar Da Shirin ASSEP A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Yadda NATO Ta Yi Amfani Da Ita A Matsayin Dalilin Neman Fadada

Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Yadda NATO Ta Yi Amfani Da Ita A Matsayin Dalilin Neman Fadada

June 26, 2025
Tinubu Ya Nemi Ƴan Nijeriya Su Taimaka A Yaƙi Shan Muggan Kwayoyi

Tinubu Ya Nemi Ƴan Nijeriya Su Taimaka A Yaƙi Shan Muggan Kwayoyi

June 26, 2025
An Yi Bikin Nune-Nunen Kayan Al’adu Na Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Italiya A Rome

An Yi Bikin Nune-Nunen Kayan Al’adu Na Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Huldar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Italiya A Rome

June 26, 2025
NNPC Ta Gaza Halartar Zaman Binciken Majalisa Kan Ɓatan Naira Tiriliyan 210

NNPC Ta Gaza Halartar Zaman Binciken Majalisa Kan Ɓatan Naira Tiriliyan 210

June 26, 2025
Tattalin Arzikin Sin Na Ci Gaba Da Ba Da Gudunmuwa Ga Habakar Tattalin Arzikin Duniya

Tattalin Arzikin Sin Na Ci Gaba Da Ba Da Gudunmuwa Ga Habakar Tattalin Arzikin Duniya

June 26, 2025
Kashim Shettima Ya Tafi Habasha Ziyarar Aiki

Kashim Shettima Ya Tafi Habasha Ziyarar Aiki

June 26, 2025
Afirka CDC Ta Yaba Da Hadin Gwiwa Kan Kiwon Lafiya Da Kasar Sin

Afirka CDC Ta Yaba Da Hadin Gwiwa Kan Kiwon Lafiya Da Kasar Sin

June 26, 2025
Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki A Janairun 2026 — Adedeji

Sabbin Dokokin Haraji Za Su Fara Aiki A Janairun 2026 — Adedeji

June 26, 2025
An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” A Italiya

An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” A Italiya

June 26, 2025
Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…

June 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.