Yanzu-yanzu rahoton da muka samu ya tabbatar da labarin rasuwar Kwamishin Ma’aikatar Ciniki Da Masana’antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari.
Majiyarmu daga Masarautar Hadejia ta bayyana cewa Kwamishinan wanda har ila yau shi ne Cigarin Hadejia, za a yi jana’izarsa a kofar fadar mai martaba Sarkin Hadejia da karfe 11:00am na safe.
Kwamishinan ya rasu ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na dare.
Rasuwar tasa dai ta haifar da gibi a Jihar Jigawa. Allah ya jikan sa da Rahama ya sa Aljannar firdausi ce makomar sa amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp