A matsayina na dan kasar waje dake kaunar al’adun kasashen Afirka, har kullum ina fatan ganin an samu ci gaban tattalin arziki a kasashen Afirka, inda hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin ya kan karfafa min gwiwar samun biyan wannan bukata.
A jiya Laraba ne, aka gudanar da wani taron karfafa zuba jari a kasar Nijar, a birnin Changsha dake tsakiyar kasar Sin. Inda wani kamfanin kasar Sin ya sa hannu kan yarjejeniyar kafa wani yankin masana’antu na musamman a kasar ta Nijar, don taimakawa kasar a kokarinta na raya bangaren masana’antu mai alaka da sarrafa amfanin gona da ma’adinai. An gudanar da wannan taro ne karkashin laimar bikin baje kolin harkokin tattalin arziki da ciniki na kasar Sin da kasashen Afirka na CAETE, wanda aka kaddamar a yau Alhamis, duk a birnin na Changsha dake kasar Sin.
A kan gudanar da bikin baje koli na CAETE a Changsha bayan ko wadanne shekaru biyu-biyu, wanda ya kasance wani muhimmin dandali, inda gwamnatoci da kamfanonin kasashen Afirka da na Sin suke mu’amala don neman kulla alakar hadin gwiwa. Bikin na bana dai ya shafi ayyuka masu alaka da gina kayayyakin more rayuwa da ba sa gurbata muhalli, da kiwon lafiya, da sarrafa amfanin gona, da gina yankunan masana’antu, da horar da matasa da ilimin sana’o’i, da sauransu. Ya zuwa yanzu wasu kamfanoni 1500 daga kasashe 29 sun tabbatar da niyyarsu ta nuna kayayyakinsu.
Haka kuma ana shirin kulla kwangiloli 218 a yayin bikin, wadanda darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 19.1. Ban da haka, kasar Najeriya na daga cikin kasashen Afirka 8 da aka gayyata a matsayin muhimman baki a bikin na wannan karo, inda za ta nuna wasu kayayyakin da ake samarwa a kasar, a wani wuri na musamman da aka kebe mata cikin dakin baje kolin kayayyaki.
Shaidu da dama sun tabbatar da yadda hadin gwiwar Afirka da Sin ke amfanar kasashen Afirka. Misali, albarkacin yadda kasar Sin ta soke harajin da ake karba kan wasu kayayyakin da ake shigo da su cikin kasuwannin kasar Sin daga wasu kasashen dake nahiyar Afirka, da sauran manufofin da Sin ta gabatar, dimbin kayayyakin kasashen Afirka, misali ganyen shayi na ti na kasar Kenya, da ridi na kasar Habasha, da dai sauransu, sun fara shiga kasuwannin kasar Sin, lamarin da ya taimaka wa manoman wadannan kasashe samun karin kudin shiga.
Bayanai na nuna cewa, ko da a kasuwar Gaoqiao dake lardin Hunan na kasar Sin kadai, an shigar da waken gahawa da darajarsa ta kai dalar Amukra miliyan 10, cikin kasar Sin, daga kasashen Afirka, a shekarar 2022. Kana ana sa ran ganin wannan adadi ya ninka a bana.
Ban da wannan kuma, wani shafin yanar gizo na sayar da kayayyaki mai taken Kilimall, da wani kamfanin kasar Sin ya kafa, yana samun karbuwa a nahiyar Afirka. Yanzu kamfanoni da daidaikun mutane fiye da 8000 na kasashen Afirka da na kasar Sin sun bude kantuna fiye da 12000 a kan wannan shafin yanar gizo, inda ake sayar da wasu nau’ikan kayayyaki kimanin miliyan 1. Kana an ce a kasar Kenya kadai, wannan shafin yanar gizo ya taimaka wajen samar da karin guraben aikin yi fiye da 5000.
Haka zalika, za a iya ganin karin nasarorin da aka cimma ta fuskar hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin a bangaren gina kayayyakin more rayuwa. Inda a kasar Najeriya, tashar jiragen ruwa ta Lekki da wani kamfanin kasar Sin ya gina za ta taimakawa birnin Legas wajen zama cibiyar jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa mafi girma a tsakiya da yammacin Afirka, kana za ta samar da sabbin guraben aikin yi kimanin dubu 200 cikin shekaru masu zuwa. A kasar Aljeriya kuma, wata tashar samar da wutar lantarki bisa zafin rana, tana samar da wutar lantarki a kai a kai ga wasu kauyukan da suke cikin hamadar Sahara. Sa’an nan a kasar Ghana, na’urorin zamani na sadarwa da aka sanya a yankunan karkarar kasar na samar da hidima ga manoman kasar fiye da miliyan 3.
Tambaya a nan ita ce, me ya sa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin Afirka da Sin ke sanya kasashen Afirka ci gaba? Amsar ita ce, shugabannin kasar Sin sun riga sun tabbatar da manufar kasar game da hadin gwiwa da kasashen Afirka, tun kusan shekaru 10 da suka wuce, wato: Kokarin zama aminiyar kasashen Afirka, da nuna musu sahihanci, da taimaka musu samun hakikanin ci gaba, gami da mai da adalci a gaban moriya yayin da take hadin gwiwa da kasashen Afirka.
Kamar yadda babban jigon bikin CAETE na wannan karo ya nuna, wato “neman samun ci gaba tare, da more wata kyakkyawar makoma a nan gaba tare”, ya nuna cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana neman hadin gwiwa tare da kasashen Afirka don su ci gaba tare. Masu iya magana na cewa da abokin daka ake shan gari, yayin da yake tafiya kan turbar neman ci gaban kasa, kuma ba zai nemi a shawo kanka, ko kuma hana ci gabanka ta hanyar daukar wasu matakai na kashin kai ba. (Bello Wang)