Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Laraba na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Faburairu, ana iya ganin tasirin saurin matakan kandagarki da yaki da annobar COVID-19 da ma manufofin kyautata tattalin arziki. Galibin alkaluman tattalin arziki sun farfado, kuma yanayin tattalin arziki gaba daya, ya nuna alamar daidaita da farfadowa.
Daga watan Janairu zuwa watan Faburairu, karin hajojin da kamfanonin kasar ke sarrafawa a cikin kasar sun karu da kashi 2.4% bisa makamancin lokaci na bara, kuma kididdigar sana’o’in ba da hidima ta kasar ta karu da kashi 5.5% cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, yayin da darajar kayayyakin masarufi da aka sayar ta kai yuan triliyan 7.7067, wanda ya karu da kashi 3.5% bisa makamancin lokaci na bara.
Kakakin hukumar kididdigar kasar Sin Fu Linghui ya bayyana cewa, a halin yanzu, wajibi ne a gaggauta aiwatar da manufofi, kuma kara kwarin gwiwar kasuwanni, inganta ci gaban tattalin arziki, himmatu wajen samun karuwar inganci mai yawa. (Safiyah Ma)