Wasu ‘yan daba a ranar Litinin sun farmaki wasu mambobin majalisar Dokokin Jihar Bauchi a gidan hutun ‘yan Majalisa da ke jihar tare da farfasa motoci da jikkata ‘yan Majalisar.Â
‘Yan daban da suka zarce mutum 50 sun mamaye gidan hutun ‘yan Majalisar a yayin da suke zaman tattaunawa, a bisa hakan sun farfasa motoci tare da tarwatsa abubuwan da ke cikin gidan.
Wannan matakin dai na zuwa ne ‘yan kasa da awanni da wasu suka yi kokarin kona Majalisar Dokokin Jihar ma, lamarin da ya tilasta wa ‘yan sanda rufe Majalisar baki daya.
Idan za ku iya tunawa dai mambobin majalisar 22 sun fara yunkurin zama domin tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y Sulaiman da sauran shugabannin Majalisar, lamarin da ya janyo rashin jituwa a tsakanin mambobin majalisar.
A yayin farmakin, an jikkata dan majalisar dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Burra, Ado Wakili.
Da yake magana da ‘yan jarida ya ce, “Muna ciki Muna zaman tattaunawa kawai muka fara jin iface-iface a waje ana Kuma buga get din. Mun fito domin mu ga meke faruwa kawai sai muka ga ‘yan daba da manyan makamai, adduna, da sauran muggan makamai.
“Mun yi kokarin tsira da lafiyar mu, a yayin hakan da dama daga cikinmu har da ni mun jikkata. Sun wargaza komai da ke cikin wajen, sun kuma farfasa mana motoci da gilasan gidan”.
Kazalika, wani dan majalisar ma, Kawuwa Shehu Damina, ya yi tir da lamarin.