A safiyar yau Laraba ne aka tashi da fargabar mutuwar mutane da dama bayan wani gini da ke unguwar Onipanu a jihar Legas ya ruguje.
An ce ginin da abin ya shafa yana kan titin Oke Arin, daura da Shyllon Ilupeju.
- Yajin Aikin ASUU: Kamata Ya Yi Buhari Ya Fara La’akari Da Rahotan Briggs —Kungiyar Iyaye
- Mataimaki: Gwamnonin APC Na Alfahari Da Zabin Tinubu – Bagudu
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1.07 na safiyar Laraba.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ta kai dauki wajen da lamarin ya faru da nufin fara aikin ceto.
Jami’an tsaro da duk masu ruwa da tsaki na aikin ceto sun kai dauki, don ceto mutane da lamarin ya rutsa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp