Kwamitin Aiki na jam’iyyar APC (SWC) na jihar Kebbi ya amince da dakatar da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Koko-Besse/Maiyama a jihar Kebbi, Hon. Shehu Muhammad Koko daga halartar ayyukan jam’iyyar.
Dakatarwar ta biyo bayan jerin korafe-korafen da kwamitin ya samu da kuma kaddamar da shi kan dan jam’iyyar daga karamar hukumarsa ta Koko-Besse kan zarge-zargen ayyukan kin jinin jam’iyyar da ya aikata, wanda hakan zai iya bata musu rai ko kuma ya haifar da wata matsala wadda ke iya sa rashin tasiri na jam’iyyar ko zama cikin ƙkiyayya, raini, izgili ko hargitsa tatsuniyoyi da ketar dokoki da ka’idoji, yanke shawara na jam’iyyar.
Hakan dukka na kunshe ne ta cikin takardar dakatarwar wadda shugaban jam’iyyar na jihar Abubakar Muhammad Kana ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Takardar dakatarwar ta ci gaba da bayyana cewa, “Shiga ayyukan rashin gaskiya, gudanar da wasu ayyukan na yaki da Jam’iyyar da ke kawo cikas ga tsarin zaman lafiya da bin doka da oda; wadanda ba su dace da manufofin jam’iyyar sabanin sashi na 21 (2) (i) (ii) (vi) (vii) (viii) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC (2022 da aka yi wa kwaskwarima).”
Don haka kwamitin ayyuka na jam’iyyar na jihar (SWC) na jam’iyyar na sanar da jama’a cewa, “Kwamitin ayyuka na jihar ya amince da dakatar da Hon. Shehu Muhammad Koko daga shiga duk wata harka ta APC har sai an kammala binciken korafe-korafen.”
Bugu da kari, an gargade shi da ya daina bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar APC, kuma kada ya shiga duk wani aiki na jam’iyyar har sai an kammala bincike.
A cewar wata majiya mai tushe ta ce Hon. Shehu Muhammad Koko a halin yanzu shi ne shugaban kwamitin rundunar sojojin sama kuma daya daga cikin na hannun daman Kakakin majalisar wakilai kuma mai goyon bayan zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.