A ranar Laraba, babban bankin Nijeriya CBN ya ce zai sauya fasalin Naira N200, N500, da N1,000.
Gwamnan babban bankin na kasa CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, inda yace, sababben kirar za su fara aiki ne daga 15 ga watan Disamba, 2022.
An dauki matakin ne domin lura da kula da yawan kudaden da ke yawo a hannun jama’a da kasuwanni, inji cewar shugaban CBN.
Emefiele ya bayyana cewa, ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na fitar da sabbin takardun kudin domin maye gurbin tsofaffun kudaden da ke yawo a kasuwanni da hannun jama’a.