A halin yanzu dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da ‘yan uwan fasinjojin da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari a ranar 28 ga watan Maris.
Taron dai ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
- Harin Jirgin Kasa: Mutane 7 Sun Samu ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga Bayan Gumi Ya Shiga Tsakani
- Jirgin Yaki Ya Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga Da Yaransa A Katsina
Idan zaku iya tunawa a ranar 28 ga Maris ‘yan bindiga sun tarwatsa hanyar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, inda suka kashe wasu tare da sace fasinjoji da dama.
Ya zuwa yanzu, kashi na biyar na wadanda abin ya shafa sun sami ‘yancinsu.