Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu, gabanin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a mako mai zuwa.
Taron ya gudana ne a fadar shugaban kasa a daren Lahadi.
- Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya Bayan Duba Lafiyarsa A Landan
- 2023: APC Ta Yi Sa’a Tinubu Ne Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa – Buhari
Taron dai na zuwa bayan da Buhari ya dawo Abuja daga birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya je duba lafiyarsa.
Idan zaku tuna cewa a ranar Talata ne jam’iyyar zata fara yakin neman zaben ta a hukumance.
A baya dai shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa zai jagoranci yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp