Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umurci bankuna da su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 daga hannun jama’a.
Sai dai babban bankin ya hana karbar kudin da ya haura sama da N500,000.
- “Akwai Masu Shekara 18 Zuwa 20 Ba Tare Da Hukunci Ba A Gidan Gyaran Hali Na Kuje”
- Karancin Kudi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga -Zanga A Legas
Tun da fari dai CBN ya bai wa bankunan kasuwanci umarnin wadata mutane da takardar tsohuwar kudin N200, biyo bayan karin wa’adin da shugaba Buhari ya yi.
Buhari ya kara wa’adin har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu wannan shekara.
Sai dai dubban mutane ne suka yi wa ofishoshin CBN a jihohi daban-daban tsinke a yau Juma’a don yi musayar kudadensu.
Amma an samu cunkoso mara misali tare da rudani a tsakanin mutane.
A Jihar Legas kuwa, zanga-zanga ce ta barke, lamarin da ya sanya Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin na Gwamnatin Tarayya.