Tijjani Ibrahim Kiyawa dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC a gundumar Jigawa ta Kudu Maso Yamma ya rasu.
Ya rasu ne a wani asibitin kasar Sin a ranar Asabar.
- Damfarar Miliyan 66: Kotu Ta Daure Maman Boko Haram Da Wasu Mutum 2
- Rashin Kula Da Tarbiyyar ‘Ya’ya Kan Zama Babbar Matsala A Gaba
An ce an kwantar da shi a wani asibitin Abuja sakamakon ciwon huhu amma an garzaya da shi kasar Sin domin ci gaba da kula da lafiyarsa a lokacin da yanayinsa ya ta’azzara.
Marigayi Kiyawa ya lashe tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC na shiyyarsa watanni uku da suka gabata.
A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya bayyana rasuwar Kiyawa a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, har da al’ummar Musulmi.
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Habibu Nuhu Kila, gwamnan ya jajanta wa iyalan mamacin.
“Gwamnan ya ce rasuwar Hon. Tijjani Ibrahim Kiyawa babban rashi ne ba ga iyalansa kadai ba har ma da al’ummar musulmi.”
“Ya bayyana marigayi Alhaji Tijjani Ibrahim Kiyawa a matsayin dan siyasa mai kishin kasa kuma rikon amana wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban siyasar kasar nan.
“Gwamna Badaru ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya masa rahama, tare da bai wa iyalansa da hakurin wannan rashi,” in ji sanarwar.
Marigayin dan siyasar ya wakilci mazabar Dutse/Kiyawa tarayya a majalisar wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.