Biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaban sabon tsarin mafi karancin albashin.
Sanarwar na zuwa ne kwanaki biyu bayan Tinubu ya bayar da umarnin gabatar da sabon tsarin mafi karancin albashi da kuma nazarin abin da ke tattare da shi.
- Hajjin Bana: NDLEA Ta Kama Maniyyata Dauke da Hodar Iblis A Legas
- Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Ci Gaba Da Biyan Tallafin Man Fetur
Rahoton na ministan kudi an ce zai zayyana wasu sabbin matakan mafi karancin albashi tare da tasirin kasafin ga gwamnatin tarayya.
Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a Litinin, domin neman karin mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati.
A gefe guda kuma ma’aikatan na bukatar janye karin kudin wutan lantarki da aka yi a baya-bayan nan.
Shugabannin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC, sun dakatar da aikin na tsawon kwanaki biyar bayan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin ci gaba da tattaunawa, tare da nemo sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan.