Gwamnan jihar Bauchi mai ci, Bala Abdulkadir Mohammed, na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.
Sakamakon zaben da jami’in zaben, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya bayyana a safiyar ranar Litinin ya bayyana cewa Gwamna Bala ya lashe zaben a kananan hukumomi 15. daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar.
- PDP Na Zargin Gwamnan Zamfara Da Yunkurin Murde Sakamakon Karamar Hukumar Maradun
- PDP Na Zargin Gwamnan Zamfara Da Yunkurin Murde Sakamakon Karamar Hukumar Maradun
Shi kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (rtd) ya samu nasara a kananan hukumomi biyar kacal na jihar.
Abubakar shine tsohon shugaban hafsan sojin saman Nijeriya.
Da misalin karfe 9:10 na safiyar ranar Litinin ne sakamakon karshe daga karamar hukumar Bauchi ya iso cibiyar tattara tattara sakamakon ta Bauchi.
Gwamna Bala ya lashe zaben a Jama’are; Kirfi; Bogoro; Warji; Itas Gadau; Shira; Zaki; Ganjuwa; Danbam; Dass; Alkaleri; Ningi; Tafawa Balewa; Toro, da kananan hukumomin Bauchi, yayin da babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar APC ya samu nasara a Giade; Gamawa; Darazo; Misau, da Katagum LGAs na Jahar.