Gwamnatin tarayya ta sauya ranar kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 da aka tsara yi a ranar 29 ga Maris, 2023.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba jim kadan bayan kammala taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar Ministan, a yanzu za a gudanar da kidayar a watan Mayu, 2023.
Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da fitar da kudi naira biliyan 2.8 ga hukumar kidaya ta kasa NPC domin sayo wasu manhajojin komfuta da za a yi amfani da su wajen gudanar da kidayar.