Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta wa ofishin EFCC kawanya, ta hana jami’an hukumar shiga ofishinsu dake Ikoyi, jihar Legas.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Premium Times cewa, jami’an tsaro na farin kaya, sun yi wa ginin ofishin EFCC kawanya tare da ajiye tankar yaki mai sulke a gaban ginin.
Hukumomin biyu a cewar rahotanni, sun dade suna takun-saka da juna kan mallakar ginin.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton, jami’an DSS sun hana dukkan jami’an EFCC da ke ofishi da ke titin Awolowo, Ikoyi shiga ginin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp