Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta bayyana sakamakon zaben gwamna na kananan hukumomi 20 na jihar bisa ga sakamakon da aka samu 388, 258 da 342, 258 da jam’iyyu biyu da suka fi kowa a zaben suka kada kuri’a.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Farfesa Yusuf Saidu na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya ce “Mun lura da inda aka soke sakamakon zaben, kuma ya nuna cewa an soke zaben a kananan hukumomi 20 na jihar daga cikin kananan hukumomi 21. RA da dama a rumfunan zabe daban-daban.
- Dan Takarar PDP, Hon. Dauda Lawal Shi Ne A Gaba A Zaben Gwamnan Zamfara
- Gwamna Buni Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Yobe
Ya kuma kara jaddada cewa, “mun hada adadin PVCs da aka tattara a rumfunan zabe, kuma ya kai jimilla 91,829 kuma a lokacin da muka duba sakamakon jam’iyyu biyu da ke kan gaba a wannan takara sun samu kuri’u 388, 258 da 342,980, wannan kuri’u inda APC mai kuri’u 388,258 da PDP mai 342,980 idan muka dubi banbancin da ke tsakanin manyan jam’iyyun biyu ya kai kuri’u 45,278.
“Mun duba dokokin zabe na shafi na 31 na dokar zabe ta 2022, sashe na 51 karamin sashe na 2 da na 3 domin neman jagora da kuma bisa ga wannan tanadi da kuma ikon da aka bani a matsayin mai tattarawa da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar a 2023 a Jihar Kebbi.
“Ni farfesa Yusuf Saidu na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar Sakkwato na bayyana zaben gwamna a jihar Kebbi wanda bai kammala ba na gode, in ji shi”.