Jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Muhammad Yushau na karamar hukumar Kura a jihar Kano ya yanke jiki Ya fadi a kofar hedikwatar INEC ta Kano, yanzu haka yana kwance a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Abokin aikinsa na karamar hukumar Garun Malam, Muhammad Shuaibu Abubakar da suka zo a mota daya da shi, zai gabatar da sakamakon zaben a madadinsa, jami’ar zabe, Maryam Adamu Abdullahi ta karamar hukumar Kura za ta taimaka masa.
Cikakkun bayanai daga baya….