Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin tarayya, Abuja karkashin jagorancin mai shari’a A.O Adeyimi, ta aike da tsohon Akanta -Janar na Nijeriya, Ahmad Idris, gidan yarin Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Yuli, 2022.
A yau ne dai EFCC ta gurfanar da tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris a gaban babbar kotu da ke Abuja, domin sauraren shari’a kan zargin almundahana da hukumar ke yi masa.
Idan ba a manta ba, a watan Mayun da ya gabata ne EFCC, ta cafke babban Akanta-Janar din bayan ya kin amsa goron gayyata da ta aike masa a lokuta daban-daban.
Cikakken rahoto na nan tafe…