Kotu ta aike da fitaccen malamin addinin a jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa zarginsa kalaman tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiya.
Malamin wanda ya amsa gayyatar ‘yansanda a ranar Litinin daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin tada zaune tsaye.
Bayanan da ke zuwa mana na cewa ‘yansandan sun gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistire ta 1.
Kotun ta tura shi zuwa gidan yarin kafin daga bisani a cigaba da sauraron karar da ‘yansanda suka shigar da shi a gobe Talata.
Da yake tabbatar da kamun da aka yi wa malamin, Shugaban kungiyar, Majalisar Matasa Masu Neman Hadin Kan Malamai Da Cigaban Al’ummar Jihar Bauchi, Yusuf A. Jibrin, ya bayyana cewar malamin ya je wajen ‘yansanda domin amsa gayyatar da suka yi masa ne amma daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu.
Ya ce: “Na san da gayyatar da aka yi wa Malam daga hukumar ‘yansanda wanda a yau da safe (Litinin) aka tabbatar mana da cewa Malam ya amsa wannan gayyatar. A da kam ma mun shirya har da ni muka ce za mu je mu yi masa rakiya. Amma da muka yi waya da Allaramma sai ya ce mana a’a malam ya ce bai bukatar kowa ya je. Zai je shi kadai da direba da Malam Ya’u.
“Dazu kuma sai shi Allaramma ya kirani yake ce min an kai Malam gidan Yari. Yake ce min har an kaishi kotu, kotu kuma ta turashi gidan yari.”
Yusuf ya ce, dukkanin abun da ake cajin malamin nasu a kai abu ne da ya shafi akidarsu, “Wannan maganar da malam ya yi akidarmu ne a kai kuma muke fatan Allah ya karbi rayukanmu, kuma manufarmu daya kuma a kanta muke.”
A cewarsa, malaminsu ya koyar da su zaman lafiya da kwanciyar hankali, don haka za su bi dukkanin matakan da suka dace a doron shari’a wajen nema wa malaminsu hakkinsa.
Shugaban, ya bayyana cewar su na ta kokarin kwantar wa almajiran malamin hankali da su kwantar da hankalinsu yayin da ake cigaba da bin matakan da suka dace wajen ganin malamin ya samu ‘yanci.
“Muna kira ga mutanenmu da su kasance cikin zaman lafiya kuma za mu bi lamarin a bisa tsarin doka domin mu tabbatar mun bi kadin abun da aka mana,” Yusuf A. Jibrin ya shaida.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa, a kwanakin baya ne Malamin na Ahlul Sunnah Dakta IdrisAbdul’aziz Dutsen Tanshi ya yi furucin cewa ‘…Ko taimakon Manzon Allah ma ba su bukata. Kafin nan ya jero sunayen wasu Shehunnan Darika inda ya nuna cewa ba a neman agajinsu a yayin neman taimako ko a lokacin da ake cikin yanayi na musifa.
Bayan yin jawabin nan nasa ne wasu ke ganin rashin ladabi wajen shigo da Manzon Allah (SAW) cikin misalinsa wanda kai tsaye wasu suka nuna hakan da rashin kimanta Manzon Allah. A kan hakan, hukumar shari’a ta jihar Bauchi ta aike da wasikar gayyata ga Malam Idris domin ya bayyana a gaban malamai domin wanke kansa ko kare kansa sai dai bayan caa da malaman da ke goyan bayansa suka yi hakan ya gagara ba tare da an samu yin wannan mukabalar ba.