Kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukunci kisa ta hanyar rataya biyo bayan samunsa da laifin yin batanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad S.A.W.
Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano.
Tun da farko Mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya ce ya gamsu da shaida da hujojjin da aka gabatar masa game da karar da ake yi wa Abduljabbar na yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.
Ya ce hujojji sun bayyana cewar Abduljabbar ne ya kirkiro dukkanin wadannan kalamai a cikin karatunsa.
Don haka kotun ta same shi da laifin aikata aifin da ake tuhumarsa da shi wanda aka shafe watanni 15 ana shari’a.
Sai dai lauyan Abduljabbar ya nemi kotun da ta yi masa sassauci saboda a cewarsa sabanin fahimta aka samu dangane da neman ilimi.
Tun da farko gwamnatin Jihar Kano ta kama Abduljabbar tare da gurfanar da shi, kan zargin yin batanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad SAW.
Daga bisani aka shirya mukabala tsakaninsa da wasu malaman jihar da suke zargin yana aikata batancin a cikin karatunsa.
Bayan yin mukabalar, Abduljabbar ya gaza kare kansa daga zargin da ake masa, wanda hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta tisa keyarsa zuwa gidan yari, inda daga nan aka ci gaba da shari’a.
Kotun a satin da ya wuce ta sanya ranar Alhamis a matsayin ranar da zata yanke hukunci bayan shafe shekara daya da wata uku ana shari’ar.
An zartar wa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin da ake zarginsa da aikatawa.