• English
  • Business News
Monday, September 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Da Dumi-Dumi: Kotun Shari’ar Musulunci Ta Tura Sheikh Idris Abdul’aziz Gidan Yari

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Da Dumi-Dumi: Kotun Shari’ar Musulunci Ta Tura Sheikh Idris Abdul’aziz Gidan Yari
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 da ke Jihar Bauchi ta tura Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa ‘raini ga kotu’ har zuwa nan da wata daya.

Alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki, shi ne ya aike da babban malamin zuwa gidan gyara halinka a zaman kotun da ya gudana ranar Litinin.

  • Wakili Ya Rasu Kwana 3 Da Karewar Wa’adinsa A Matsayin Dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

A kwafin umurnin aikewa da Malamin gidan yari da wakilinmu ya ci karo da ita da ke nuni da cewa bisa ga ‘raini ga kotu’ wato ‘Contempt of court’ ne Alkalin ya aike da malamin gidan yari, inda za a da dawo da shi gaban kotun a ranar 19 ga watan gobe.

Umurnin da Alkalin ya bai wa babban jami’in kula da gidan yarin na cewa, “An baka izinin ka karbe shi ka tsare shi a gadirum sai an aiko maka da wata oda.”

Umarnin na kotun ya ce idan har ba wata umarnin na daban kuma aka aiko ba, malamin zai cigaba da zama a gidan har zuwa ranar 19/07/2023.

Labarai Masu Nasaba

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

Idris Abdul'aziz
Takardar shaidar kotun da ta tura Dr. Idris Abdulaziz gidan yari

Idan za a tuna dai, a ranar Laraba 31 ga watan Mayun 2023 ne dai Alkalin kotun ya umarci jami’an tsaro da su kamo malamin a duk inda suka gan shi sakamakon kin bayyana a gaban kotu.

Sai dai a zaman kotun a ranar 5 ga watan Yuni malamin ya bayyana a gaban alkalin inda lauyoyinsa suka gabatar da rahoton likita da ke cewa bai zo kotun ba ne sakamakon rashin lafiya da ke fama da ita.

Bayan da lauyoyin nasa suka gabatar da rahoton, sun roki kotun da ta janye tare da jingine umarnin da ta bayar na farko na cewa a kamo malamin duk aka gan shi. Sai dai Alkalin ya daga zaman zuwa yau don yanke hukunci kan bukatar.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan hukunci, daya daga cikin Lauyoyin malamin, Barista Kamal A. R Muhammad, ya ce, su na nazarin halin da ake ciki domin daukan matakin da ya dace na nema wa malamin ‘yanci.

A cewarsa: “Da farko an dawo kotun ne domin a saurari bukatarmu na neman a kori karar saboda da hujjarmu na cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Na biyu kuma akwai rokon da muka yi na cewa umarnin da kotun ta yi a ranar farko na a nemo malam a tsareshi saboda bai zo kotu ba a jingine don mun gabatar da rahoton asibiti da ke cewa baya da lafiya.

“Kafin yau din ma, mun shigar da daukaka kara da muke neman a canza shari’ar zuwa wata kotu da take da hurumi zuwa gaban alkalin da ke da hurumi, sai Alkalin ya ce ba zai kori karar ba don yana da hurumin sauraron wannan karar.”

A cewar Lauyan, “Yanzu dai halin da ake ciki Alkalin ya ce a kai Malam zuwa gidan yari har zuwa ranar 19 ba watan Yulin 2023.”

Barista Kamal malamin ya ce akwai matakan da za su dauka na nuna korafinsu kan wannan lamarin.

LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa, tun da farko dai, ‘yansanda ne suka fara gabatar da malamin a kotun majistire bisa zarginsa da laifin tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiyan al’umma, lamarin da ya kai ga zuwansa gidan yari na tsawon mako guda amma daga bisani ya samu beli.

Kodayake ma’aikatar shari’a ta Jihar Bauchi ta amshi ragamar shari’ar daga baya.

Sai dai kuma bayan fitowarsa ne aka sake mayar da shari’ar da ake masa daga kotun majistiren zuwa kotun shari’ar Musulunci.

Wakilinmu ya ce, zuwa yanzu haka dai malamin wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi na tsare a babban gidan gyara halin da ke Bauchi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaba Xi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Next Post

Maimakon Yaki, Afirka Da Sin Sun Zabi Zaman Lafiya

Related

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
Manyan Labarai

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

11 minutes ago
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara
Labarai

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

1 hour ago
An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya
Labarai

An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya

13 hours ago
Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Manyan Labarai

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

14 hours ago
Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara
Labarai

Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

16 hours ago
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi
Labarai

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

17 hours ago
Next Post
Maimakon Yaki, Afirka Da Sin Sun Zabi Zaman Lafiya

Maimakon Yaki, Afirka Da Sin Sun Zabi Zaman Lafiya

LABARAI MASU NASABA

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

September 15, 2025
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

September 15, 2025
Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

September 15, 2025
Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)

September 14, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Madrid

Sin Da Amurka Sun Fara Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Madrid

September 14, 2025
An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya

An Gano Gawar Yarinyar da Ruwan Sama Ya Tafi Da ita A Zariya

September 14, 2025
Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana

September 14, 2025
Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya

Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya

September 14, 2025
Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Lauyoyi Biyu Sun Janye Daga Kai Jaafar Jaafar Ƙara, Sun Ce An Sanya Sunayensu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

September 14, 2025
Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.