Sakatariyar harkokin wajen Burtaniya, Liz Truss, ta zama shugabar jam’iyyar Conservative mai mulki kuma sabuwar Fira minista inda ta karbi ragamar mulki daga tsohon Fira ministan Burtaniya, Boris Johnson a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tsadar rayuwa, durkushewar masana’antu da kuma koma bayan tattalin arziki.
Bayan makonni na takarar shugabancin jam’iyyar mai cike da rudani da rarrabuwar kawuna tsakanin magoya bayan ‘yan takarar, Truss da Rishi Sunak, tsohon ministan kudi.
A watan Yuli ne aka tilastawa Johnson ya sanar da murabus din nasa bayan shafe watanni gwamnatinsa na fuskantar suka da tsangwama daga bangarori daban-daban.
Bayan ayyana Truss a matsayin Sabuwar Fira minista, ana sa ran, Johnson zai tafi Scotland domin ganawa da Sarauniya Elizabeth ranar Talata domin mika murabus din nasa a hukumance.
Ta dade akan gaba a gwagwarmayar maye gurbin Johnson, Truss ta zama Fira minista ta hudu ta Jam’iyyar Conservative tun zaben 2015.