Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato, Hon. Yakubu Yalson Sanda ya sha kaye a mazabarsa a hannun jam’iyyar PDP a zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a ranar Asabar.
‘Yar takarar jam’iyyar PDP, Misis Happiness Matthew Akawu, ce ta lallasa Kakakin Majalisar a kujerar dan majalisar jiha da ke wakiltar mazabar Penhana.
- Wadanda Za Su Fadi Zabe Ne Ke Neman Hargitsi A Zamfara -Lawal Dare
- An Harbe Tsohon Kansila Har Lahira Kan Zargin Sace Akwatin Zabe A Kano
Misis Akawu ta samu kuri’u 9,926 inda ta kayar da babban abokin hamayyarta Rt. Hon. Sanda na jam’iyyar APC da ya samu kuri’u 7,936.
Kazalika, Hon. Faisal Haruna Maitala na jam’iyyar PRP ya samu kuri’u 6,721 yayin da kuma Hon. Dankama na Labour Party ya samu kuri’u 1,028.
An bayyana Misis Happiness Matthew Akawu a matsayin wacce ta lashe zaben da kuri’u masu rinjaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp