Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin shekarar 2024.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mataimakiyar daraktan hukumar kan harkokin jama’a da yada labarai, Fatima Sanda Usara ta ce, sabon wa’adin shi ne 31 ga watan Janairu, 2024 maimakon 31 ga Disamba, 2023.
- ‘Yan Sa-kai Za Su Taka Rawa Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya – Yusha’u Kebbe
- Matatar Dangote Ta Karbi Danyen Mai Karo Na 4 Daga NNPC
Ta kara da cewa, “an tsawaita wa’adin ne biyo bayan kiraye-kiraye da malaman addini, Hukumomin jin dadin Alhazai na Jiha, Gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka yi.”
Usara ta bayyana cewa, amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na tsawaita wa’adin ya ba da dama ga maniyyata su bada himma wajen biyan kudin zuwa aikin hajjin mai alfarma.