Dan gani kashenin Atiku Abubakar, Sanata Abdul Ahmed Ningi ya lashe zaben kujerar Sanatan Bauchi ta tsakiya a zaben ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar.
Da ya ke ayyana sakamakon zaben a Darazo a daren ranar Lahadi, babban baturen tattara sakamakon zabe, Farfesa Ibrahim Muhammad Danjuma ya shelanta cewa Ningi na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 104,878 yayin da kuma Uba Ahmed Nana na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 84,621.
Farfesa Ibrahim Danjuma ya kara da cewa Sanata Isa Hamma Misau na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 17,995.
A bisa gamsuwa da ya yi da sakamakon zaben, ya ayyana cewa Abdul Ningi ya lashe zabe kuma ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp