Shugaban hukumar kula da ‘yansandan Nijeriya (PSC), Musiliu Smith ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan rashin jituwa da kai ruwa-rana da aka yi ta samu a tsakanin hukumar da Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, dangane da batun daukan sabbin ‘yansanda, karin girma wa jami’ai, daukan Kwansitabul da wasu jami’ai.
Lamarin har ta kai Majalisar koli na hukumar ta bukaci Smith da ya yi murabus cikin ruwan sanyi kuma ya amince da yin haka.
Smith, wanda tsohon Sufeto Janar na ‘yansanda ne, ana sa ran zai mika ragamar mulkin hukumar ga Justice Clara Ogunbiyi (Mai ritaya) wanda shi ne wakilin sashin shari’a a hukumar.
Kakakin hukumar kula da harkokin ‘yansandan Nijeriya, Ikechukwu Ani, ya tabbatar da ajiye aikin Mista Musiliu Smith a ranar Laraba.
LEADERSHIP Hausa ta nakalto cewa an dauki ‘yan kwanaki ana kai ruwa rana a tsakanin bangarorin biyu wanda a dokance hukumar ce ke da damar gudanar da aikin daukan ‘yansanda.
Ita dai PSC ta wallafa tallar daukan sabbin jami’an ‘yansanda masu mukamin Kwansitabul (constables) tare da bukatar masu sha’awar nema da su cika bukatar hakan a shafinta.
Sai dai kuma daga baya rundunar ‘yansanda ta nemi jama’a da su yi watsi da wannan sanarwar, ta kage kai da fata cewa shirye-shiryen daukan ikonta ne.
Bisa wannan rashin jituwa da fahimtar juna da aka samu, a ranar 24 g watan Agustan, hadakar kungiyar hukumar kula da ‘yansanda suka ayyana tafiya yajin aikin sai baabaa ta gani ga hukumar gudanarwa dangane da abun da suka kira saba yarjejeniya.