Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da dakatar da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) Mr. AbdulRasheed Bawa, CON, na har illa-masha Allah domin ba da cikakken damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa ofishinsa.
A cewar wata sanarwa a ranar Labara da ta fito daga ofishin sakataren Gwamnatin tarayya, wannan matakin na zuwa ne bayan zarge-zargen da ake yi wa Bawa na cin amanar ofishinsa ta hanyar kauce wa ka’idar aiki.
An kuma umarci Bawa da ya gaggauta mika ragamar ofishin nasa ga darakta mai kula da sashin ayyuka na hukumar domin cigaba da kula da harkokin hukumar har zuwa lokacin da za a kammala gudanar da bincike.
Cikakken labari daga baya:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp