Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata, wanda ya kawo ƙarshen tattaunawa tsakanin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin Ƙwadago da kuma kamfanoni masu zaman kansu, tare alƙawarin sabunta dokar duk bayan shekaru uku.
A yau Litinin, ne shugaba Tinubu, ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya inda shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranci tawagar majalisar zuwa bikin rattaba hannu kan ƙudirin dokar.
- Ko Kun San Sabbin Kwamitin Gudanarwar Kano Pillars Da Gwamnatin Kano Ta Nada?
- Zanga-zanga: Za Mu Yi Amfani Da Dandalin Eagle Square Ko Da Izini Ko Babu A Abuja
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin Ƙwadago sun cimma yarjejeniya kan ₦70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na kasa, inda shugaban ya aika da ƙudirin dokar ga majalisar dokokin, wanda aka yi gaggawar zartar wa a makon jiya.
Shugaban ma’aikatan tarayya, Dakta Yemi Folade-Esan, ta ce babu shakka sabuwar dokar za ta tabbatar wa ma’aikata cewa shugaba Tinubu, ya damu walwalar su tare da godewa Majalisar kan yadda ta gaggauta tabbatar da dokar.