Wasu ‘Yan bindiga da ake sun kashe babban jami’in ‘Yan sanda (DPO) na Paiko, SP Mukhtar Sabiu da wasu ‘yan sanda hudu a jihar Neja.
Binciken LEADERSHIP ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai hari a kasuwar kauyen Chibani ta Sarkin-Pawa da ke karamar Hukumar Munya ta Jihar da kuma kai wa DPO na Paiko da Gurara domin fatattakarsu a lokacin da lamarin ya faru.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp