Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zurak da kuma kauyen Bankalala da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase a Jihar Filato, inda suka kashe mutane sama da 40, ciki har da ‘yan banga tare da raunata wasu.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewar ‘yan bindigar sun kuma kone gidaje da dama a kauyukan.
- Toni Kroos Zai Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa Bayan Gasar Euro
- Liverpool Ta Bayyana Arne Slot A Matsayin Wanda Zai Maye Gurbin Klopp
A cewar wani mazauna yankin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Litinin, amma ba su kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro ba.
Wani shugaban matasan yankin, Sahpi’i Sambo, wanda ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun isa unguwar ne a kan babura, biyu kan keke, dauke da manyan muggan makamai, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
“Sama da mutane 40 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata, mazauna kauyen sun gudu zuwa makwabtan kauyuka domin samun mafaka, har zuwa jiya jami’an tsaro ba su zo ba,” in ji Sambo.
Da yake tabbatar wa wakilinmu faruwar harin, jami’in yada labarai na karamar hukumar Wase, Daniel Manwan, ya ce an kashe sama da mutum 30 a kauyen Bankalala yayin da jami’an DSS suka yi nasarar kashe uku daga cikin ‘yan bindigar a kauyen Zurak.
“Yayin da nake magana da kai, duk kauyukan sun zama ba kowa saboda tsananin tsoro da fargaba,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai ce uffan kan faruwar harin ba.