Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon sakataren gwamnatin Jihar Enugu, Dakta Dan Shere da wasu adadin mutanen da har zuwa yanzu ba a san adadinsu ba.
An nakalto cewa, Mista Dan na daga cikin matafiya da dama da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Enugu-Ugwuogo zuwa Nike-Nsukka a ranar Alhamis.
- ‘Yansanda Sun Kama Wani Mutum Da Katin Zabe Sama Da 100 A Sakkwato
- Kisan Kai: Kwamishinan ‘Yansanda Ya Bada Umarnin Yin Bincike Kan Mutuwar Jami’in Dansanda A Kebbi
Dakta Dan ya yi aiki ne a karkashin gwamnatin gwamna Chimaroke Nnamani.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, Shere, kwararren likita ne, ya yi tafiya ne zuwa Nsukka domin halartar ganawa a yayin da ya ci karo da ‘yan bindigar da suka farmakesu shi da sauran matafiya.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar da yawansu ya haura takwas ne suka kaddamar da wannan harin, kuma sun yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su sace mutanen.
“Sun yi ta harbin motocinmu; daya daga cikinmu ma harsashi ya same shi. Amma direbanmu ya yi kokari ya arce. Mun samu nasarar kai wanda aka harba zuwa asibiti,” a cewar daga daga cikin fasinjojin da suka tsira.
A wani labarin makamancin wannan, wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da mutane a ranar Lahadi suna ta kara kudin karbar fansa.
“Da farko sun nemi diyyar miliyan biyu na mutum daya daga cikin wadanda suka sace, amma daga baya suka sauya farashi, yanzu kuma sun kara har zuwa miliyan 30.
“Sun yi ta binciken wayoyin wadanda suka sace din ne domin gano ko su waye da irin girmansu,” a cewar majiya.
Sannan, daliban Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka da aka yi garkuwa da su a ranar Lahadi har yanzu suna tsare a hannun masu garkuwar.