A kokarinta na yaki da miyagun laifuka, Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sake dakile wani yunkurin yin garkuwa da kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Rt. Hon. Yakubu Sanda.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo ya fitar a garin Jos, ya ce wasu ‘yan bindiga uku da ba a san ko su wanene ba, sun salallabo cikin wata mota kirar CR-V Jeep mai launin ruwan toka, sun kutsa kai gidan kakakin majalisar da ke rukunin gidaje tarayya a karamar hukumar Jos ta Kudu. ranar Alhamis.
- Dan Majalisar Dokokin Jihar Legas, Abdulsobur Omititi Ya Rasu A Wajen Taron Tinubu A Jos
- Bayan Ruwan Wuta: Masu Garkuwa Sun kama Basarake A Jos
Ya bayyana cewa, bayan sun bi sawun shugaban majalisar zuwa gidansa, masu garkuwar sun yi yunkurin shiga gidansa domin yin garkuwa da shi, amma abin ya ci tura sakamakon ‘yan sandan da ke aikin gadi a gidan sun fatattaki maharan.
Alabo ya kuma kara da cewa, rundunar ‘yan sandan na ci gaba da kokarin zakulo wadanda ake zargi da tare da gurfanar da su a gaban Kotu.
Kakakin rundunar ya godewa jama’a da suka nuna damuwarsu game da abubuwan da ke faruwa a wurare daban-daban da kuma sadaukar da kai wajen baiwa ‘yan sanda bayanai kan lokaci domin daukar matakin gaggawa.
Ya kuma bukaci Jama’ar Jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba domin kuwa tuni ‘yan sanda suka yi kokarin tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa a fadin Jihar.
Kakakin ya kuma bayyana cewa za su ci gaba da dakile munanan ayyuka ta hanyar amfani da dabaru wajen dakile miyagun laifuka a jihar.